Tarihin ilimin kur'ani

Bincike akan kur'ani da bincike akan bangarorinsa dabab-daban ya fara ne tun farkon karnin farko kuma ya cigaba ya zuwa yanzu kuma zai  cigaba din. manya-manyan masana na musulunci sun yi aiki a wannan fage kuma sun  rubuta littafai da dama akan hakan.

  Bisa dogaro da dalilan dake hannu sun tabbatar da cewa wanda ya fara bahsi akan kur'ani shi ne. Yahya bin Ya'mur wanda yake almajiri ne ga Abul Aswad du'uli Sahabin Imam Ali a.s. wanda ya rasu shekara ta 89 bayan hijra.Ya rubuta  littafi ne a kan Kira'o'i daban –daban na wannan lokaci.Sannan sai Hasanu busari wanda ya yi wafati a shekara ta 110 bayan hijra, ya rubuta littafi akan yawan ayo yin kur'ani maigirma.

Marubuta da littattafan da aka rubuta a wannan fage su ne kamar haka.:Abdullahi bn Amir Yahsabi, wanda ya yi wafati a shekara ta 118H.ya rubuta littafi akan sabani akan kur'anan Usmani(mushafi usmani) sannan da wani akan Wakf da wasl a cikn Kur'ani mai girma.

 Sannan sai Shaiba bn Nisah madani wanda ya yi wafati a shekara ta 130H. Shi ne mutum na farko  bayan Yahya bn ya'amur da ya rubuta littafi a kan Kira'a.

Muhammad bn Sa'aib Kalbi wanda ya yi wafati a shekara ta 146H. Shi ne mutum na farko da ya rubuta likttafi akan hukunce-hukuncen kur'ani (Ahakam kur'an)

Makatil bn Sulaiman wanda ya yi wafati a shekara ta 150H. Shine marubuci na farko da ya yi rubutu a kan ayoyi masu kamanni(ayaat mutashabihat).

 Abu Amru Ala' bin Zuban Tamimi wanda ya yi wafati a shekara ta 154 ya rubuta littafi akan Farawa da tsayawa wajen karatun kur'ani(wakf wa ibtidaa).

Sannan sai Hamza bn Habib wanda shi ne  daya daga cikin masu kira'o'i bakwai, ya rubuta littafi akan fannin Kira'a. Ya yi wafati 156H.

 Sannan sai Yahya bn Ziyad Farra'a ya yi wafati shekara ta 207, ya rubuta littafi akn Ma'nar Kur'ani yana da mujalldi uku.wannan maruci kuma ya rubuta litttafi akan sabanin yan Kufa,Basara da Sham akan mushaf, sannan ya rubuta littafi akan Jam'i da kuma abu guda biyu a cikin kur'ani.

 Muhammad bn Umar Wakidi wanda ya yi wafati a shekara ta 207H. Ya rubuta littafin akan ilimin kurani da kuma littafi akan kura-kuren masu ruwaya.

 Sannan sai Abu mu"umar bn musanna wanda ya yi wafati a shekara ta 209H. Ya rubuta littafi akan mu'ujizar kur'ani a cikn mujalladi guda biyu. Sannan ya rubuta littafin Ma'anonin kur'ani. Shi ne mutum na farko da ya yi rubutu akan mu'ujizar kur'ani.

 Sannan sai Abu Ubaid Kasim bn Salam wanda ya yi wafati a shekara ta 224 ya rubuta littafai da dama akan ilimin kur'ani, shi ne mutum na farko da ya rubuta littafai da suka yi bayani mai zurfi akan wannan fage.

 Daga cikin littafansa fadha'ilul kur'an, Nasikh wa mansukh, Almaksurul mamdud, garibul kur'an da dai sauransu.

  Sai Ali bn Madini wanda ya yi wafati a shekara ta 234

Ya rubuta littafi a kan dalilin saukar da sururi da ayoyin kur'ani.

 A karni na takwas ne a ka rubuta littafi cikakke akan ilmin kur'ani, wannan littafi Babban masanin nan ne ya rubuta shi wato Imam Badruddin Muhammad bn Abdullah Zarkeshi ya rubuta shi. Ya yi wafati a shekara ta 794H. wannan littafi shi ne Alburhan fi Ulumil Kur'an a cikin wannan littafi ya yi bincike akan fannonin ilimin kurani har arba'in da bakwai.

  Sannan sai karni na tara shima an rubuta muhimmi kuma mashahurin littafin akan ilimin kur'ani, wato itkan fi ulumil kur'an, wanda mashahurin malamin nan wato Jalaluddin Suyudi ya rubta. Wanda ya yi wafati a shekara ta 911H.

 Wadan nan kadan kenan daga cikin littafan da aka rubuta ko aka yi bincike akan Alku'ani maigirma . Bayan wannan kuma akwai wadan su malaman tafsir sun kawo wadansu bahsoshin a farkon tafsiransu wanda suka shafi ilimin kur'ani a matsayin gabatarwa ga tafsirinsu.

  Wadannnan malami kuwa su ne kamar su Ragib Isfahani a cikin tafsirinsa mai suna Jami'ut tafasir a farkon wannan tafsiri  ya kawo bahsi mai kawatarwa a kan  ilimin kur'ani.

Haka nan a cikin Tafsirin Ibn Adiyya ya kawo irin wannan bahsin a farkon tafsirinsa.

 Haka nan a cikin Tafsirin Kurdabi da ibn kathir da tafsirin dabri,duk sun kawo irin wannan bah'sin maigamsarwa a farkon tafsirinsu.

 Sannan daga cikin malaman wannnan zamanin akwai malaman da suka yi rubutu,a wannan fage kuma suna da littafai muhimmai a wannan fage. Kamar mashahurin malamin nan wato khu'i yana da littafi a kan ilimin Kur'ani mai suna Albayan, yana daya daga cikin littafai da ake dogara da su a cikin wannan fanni.

 Sannan akwai Mashahurin malamin nan wato Ayatullahi Hadi Ma'arifa  yana da wani muhimmin littafi akan wannan fage mai suna Attamhid . wadan nan littafai suna da  muhimmancin gaske ya kamata mutum ya same su domin ya ga abin da suka kunsa na ilimi.

 Sannan sai gabatarwar tafsiril Safi na kashani da gabatarwar atfsirulBurhan na Tabarasi, gabatarwar tafsirin Tibyan duk suna daga cikin tafsiran da a cikin gabatarwarsu suka yi cikakken bayani akan ulumul kur'an a matsayin gabatarwa a cikn tafsirinsu.

  Saboda haka manya-manyan littafai da ake komawa wajensu akan abin da ya shafi  Ilmin kur'ani babu kamar Alburhan na Zarkashi da Al'itkan na Jalaluddini suyudi, da fata zamu bada lokacimmu domin fa'idantuwa da wadan littafai masu albarka.